
Hukumar
dake kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR ta ce
kawo yanzu mutane 40,000 ne su ka gujewa rikicin Boko Haram a Nigeria su
ka tsallaka zuwa makwabciyar kasar Niger.
Jami'in hukumar a Jamhuriyar Niger wanda ya
bayyanawa BBC hakan, ya ce za su tallafawa dubban 'yan gudun hijirar
musamman wanda ke zaune a yankin Diffa.
Abubakar Shekau na Boko Haram
Mutanen wadanda suke cikin mawuyacin hali sun yada zango ne a garuruwan Geskerou, Diffa, Toumour, Nguelkolo da kuma Chetimari.
'Tallafin Red Cross'
Sakamakon yanayi marar dadin da 'yan gudun hijirar ke ciki, kungiyar agaji ta Red Cross a Jamhuriyar Niger, ta ce daga watan Mayun 2012 zuwa yanzu ta bada tallafi ga dubban mutanen da suka gujewa yakin.

Sojojin Nigeria na sintiri a cikin birnin Maiduguri
Rikicin Boko Haram musamman a arewa maso gabashin Nigeria ya janyo rasuwar daruruwan mutane tare da barnata dukiya ta miliyoyin kudi.
Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan ya kafa dokar ta-baci a jihohin Borno da Yobe da Adamawa a kokarin kawo karshen zubar da jinin da ake yi.
Sai dai rahotanni sun nuna cewar duk da irin matakan da gwamnati ta ce ta na dauka don kawo zaman lafiya, har yanzu 'yan Boko Haram na samun damar kai hare-hare a yankin.
No comments:
Post a Comment